✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dillalan masu gidajen man fetur sun yi zang-zangar lumana a Kaduna 

A yau Talata ne shugabannin kungiyar masu gidajen man fetur suka yi zanga-zangar lumana a ‎kamfanin man fetur na kasa da ke jihar Kaduna, saboda…

A yau Talata ne shugabannin kungiyar masu gidajen man fetur suka yi zanga-zangar lumana a ‎kamfanin man fetur na kasa da ke jihar Kaduna, saboda nuna rashin jin dadinsu ga yadda ba’abin ka’ida wajen jigilar mai a kamfanin.

Dillalan sun nuna cewa, akan nuna sankai tare da yin alfarma wajen yin dakon man fetur a kamfanin wanda hakan ke sa a danne hakkinsu daga cikin membobinsu.

Shugaban kungiyar Dillalan Kwamrade Abdulfatahi Multala, wanda shi ne ya jagoranci sauran ‘yan kungiyar zuwa kamfanin ta KRPC a Kaduna ya bayyana cewa, ba za su yarda a rika nuna san kai tare da kin bin dokoki wajen yin jigilar man fetur ba a kamfanin.

“Dalilin zuwan mu nan wajen shi ne domin muna kin amincewa da zalunci da ake neman yi a wannan kamfani na matatar mai da ke Kaduna. Ba zamu yarda da zalunci ba. An ce babu man fetur amma kuma an aiko da takarda daga Abuja cewa, a bai wa wani mutum motoci takwas kenan dai akwai mai a kamfanin.

“Bamu ce kada a yi alfarma ba amma akwai motoci kusan bakwai da suka yi kwante suna jiran a basu mai amma ba’a basu ba kimanin watanni biyu kenan suna jira. Kuma sun biya kudadensu amma har yanzu ba’a basu kaya ba. Dan haka muke nuna rashin jin dadinmu.” In ji shi.

Ya kuma mika godiyarsa ga sauran ‘yan kungiyar irin su kungiyar direbobin tankar mai watau PTD  da sauransu abisa goyan baya da suka basu na hana a yi jigilar mai a kamfanin.

‎A jawabinsa shugaban wannan yanki na NUPENG Kwamrade Ahmed Tijjani, ya bayyana goyan bayansa ga wannan zanga-zanga da dillalan masu gidajen man fetur suka yi inda ya ce, a shirye suke su tabbatar da an tsayar da adalci a kamfanin.

“Muna nan zamu tattauna da duk wadanda abin ya shafa domin ganin a tsayar da adalci domin a gaskiya babu adalci a ce mutum ya biya kudinsa na tsawon lokaci amma a hana shi lodi dan haka zamu bincika muga su waye suka aiko da takardar idan ya kama mu gama da Janar Manaja na NNPC ne zamu nemi yin hakan domin a magance matsalar,” in ji shi.

Ya kuma tabbatarwa da masu zanga-zangar cewa, ‎duk masu ruwa da tsaki za’a nemi su domin magance matsalar a kamfanin.

A kokarin jin tabakin hukumomin kamfanin KRPC a Kaduna ya ci tura domin sun nuna ba zasu ce komai ba sai dai a tuntubi Abuja.