✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kamfanin Media Trust ya ba babban dillalansa mota… Jaridun kamfanin aka fi saya a Arewa kuma na biyu a kasa baki daya

Mahukuntan Kamfanin Media Trust mai buga jaridun Daily Trust da Weekly Trust da Sunday Trust da kuma Aminiya sun ba da kyautar sabuwar mota kirar…

Farko daga dama Manajin Daraktan kuma Babban Jami’in Gudanarwa na Kamfanin Media Trust , Alhaji Isiaq Ajibola yana mika mabudin sabuwar mota qirar KIA PICANTO ga Bala Yaro, na biyu daga hagu bayan ya zama babban dillalin jaridun kamfanin a wurin taron shekara-shekara na sashin kasuwanci da aka gudanar a Abuja.  Na biyu daga dama Mataimakin Darakta Bangaren Kasuwanci ne Alhaji Aliu Akoshile.Mahukuntan Kamfanin Media Trust mai buga jaridun Daily Trust da Weekly Trust da Sunday Trust da kuma Aminiya sun ba da kyautar sabuwar mota kirar KIA Picanto ga daya daga cikin dillalanta mai suna Bala Yaro daga Jihar Kano, bayan da ya zama babban dillalan kamfanin da ke biyan kudinsu a hannu kafin karbar jaridun.
Manajan Daraktan kuma Babban Jami’in Gudanarwar Kamfanin Alhaji Isiak Ajibola ne ya mika mabudin motar ga Bala Yaro a wajen taron shekara-shekara na bangaren kasuwanci na kamfanin a ranar Asabar da ta gabata inda ya ce wannan wani bangare ne na yunkurin kamfanin na sakayya da kuma tafiya da dukkan abokan huldarsa.
Alhaji Ajibola, wanda ya bayyana cewa wani bincike da wata cibiya mai suna Media Reach kan jaridun kasar nan na shekarar 2012 ya nuna cewa jaridar Daily Trust ce ta biyu a cikin jaridun da aka fi saye a kasar nan kuma ita ce ta daya a Arewa, don haka ya nemi masu ruwa da tsaki su hada hannu domin dada daga martabar kamfanin.
Ya ce kamfanin yana shirin kafa madaba’a a Legas a kokarinsa na fadada isar da jaridunsa ga jama’a a daukacin kasar nan.
Manajan Daraktan wanda tun farko ya nemi afuwa kan kasa gudanar da taron a bara, ya yi alkawarin mayyar da shi na shekara-shekara. Ya ce ana gudanar da taron ne domin karfafa kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin masu ruwa da tsaki na jaridun tare da magance wasu matsaloli da ka iya tasowa domin amfanin juna, ya ce ta irin wannan hanya ce za a iya samu kyakkyawar fahimta da ci gaba.
Ya gode wa dillalan jaridun kan sadaukar da kawunansu ga kamfanin, inda ya bayyana sabon tsarin “biya a ba ka,” a matsayin “wata dabara ta karfafa kasuwancin dukkan bangarorin.” Ya tabbatar wa dilallai da masu sayar da jaridun kamfanin ci gaba da samun goyon bayan kamfanin, tare da alkawarin cewa kamfanin zai fara rarraba musu jakunkunan leda da za su taimaka musu su rika sayyar da jaridun koda ana ruwan sama.
A jawabin Mataimakin Darakta bangaren Kasuwanci da Dabaru na Kamfanin, Alhaji Aliu Akoshile, ya bukaci abokan huldar kamfanin su rungumi sabon tsarin harkokin kudi da Babban Bankin Najeriya ya bullo da shi domin saukaka harkokin kasuwanci ta amfanin da hanyoyin zamani.
Ya ce kwanan nan kamfanin zai bullo wa dillallan da hanyar biyan kudi cikin sauki, inda ya ce kamfanin yana dada bunkasa domin haka su yi amfani da wannan dama domin cin gajiyar fadadar da kamfanin yake yyi.
Zakarar babbar kyautar Malam Bala Yaro ya gode wa mahukuntan kamfanin kan karramawar da suka yi masa bisa lura da kwazonsa, kuma ya yi alkawarin ci gaba da kasancewa mai sadaukar da kai ga kamfanin.
Dillalin ya bukaci abokansa dillalai su kasance masu gaskiya da sadaukar da kai ga Kamfanin Media Trust, inda ya ce shi ne kadai kamfanin buga jaridu da ke kula da sauran masu ruwa da tsaki a harkokin kasuwancin jaridu.
A yayin bikin an ba da babura biyu ga wasu dillalai da suka hada da Bashir Hussaini da Ibrahim Shittu, wadanda suka zo na biyu da na uku wajen sayar da jaridun ta hanyar ‘biya a ba ka.’  Sannan an raba wasu kyaututtuka 15 ga wasu dillalan da suka fito daga sassan kasar nan.