✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manoman Filato sun noma shinkafa eka dubu 10 karkashin shirin Fadama III

Shugaban shirin Fadama III a Jihar Filato, Mista Gideon Dandam ya bayyana cewa manoman Jihar Filato karkashin shirin Fadama III mutum dubu 10 ne suka…

Shugaban shirin Fadama III a Jihar Filato, Mista Gideon Dandam ya bayyana cewa manoman Jihar Filato karkashin shirin Fadama III mutum dubu 10 ne suka noma shinkafa eka dubu 10 a daminar bana. Mista Gideon Dandam ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da jaridar Aminiya a farkon wannan makon.

 Ya ce a wannan shiri na Famada III a jihar ta Filato, tun da farkon damina an tallafawa manoman ta hanyar yi wa kowanne manomi kaftu a gonarsa da ba shi irin shinkafa ingantatce da maganin kashe ciyawa da takin zamani buhu hudu na NPK da buhu biyu na Uriya a kan kowace eka daya, tare da koyawa manomin yadda ake noma shinkafar. 

 Ya ce kananan hukumomin jihar ta Filato  da aka yi wannan noman shinkafa sun hada da Mangu da Pankshin da Kanke da Wase da Langtang ta Kudu da Langtang ta Arewa da Kanam da Shendam da kann Pan da Mikang da Bassa da Jos ta Gabas da kuma Barikin Ladi.

 “Ya zuwa yanzu shinkafar da manoman suka noma ta yi kyau sosai da sosai, don haka manoman suna ta murnar ganin irin dimbin shinkafar da zasu samu. Kuma tuni sun kulla yarjejeniya da wani kamfani mai suna Tim Tali Rice Mill da zai sayi shinkafar ya sarrafa ta’’. 

 Shugaban shirin na Fadama ya yi bayanin cewa babu shakka wannan Shinkafa da manoman jihar Filato suka noma, idan ta zo, ta fi karfin al’ummar jihar, dole sai dai a fitar da ita zuwa wasu jihohin kasar nan.

 Ya yi kira ga gwamnatin jihar Filato da sauran masu hannu da shuni su kafa manyan injinan sarrafa shinkafa a Jihar Filato, domin shinkafar da manoman suka noma tafi karfin kamfani daya ya iya sarrafata.

 Daga nan ya yabawa shugaban kasa Muhammad Buhari da Gwamnan Jihar Filato Simon Lalong kan kokarin da suka yi wajen tallafawa harkokin noma.